HAU112: Introduction to Hausa Linguistic II
Wannan kwas ya himmatu ne wajen bayyana batutuwan da suka shafi al‟adun zamantakewar Hausawa. A cikin muhimman batutuwan kuwa sun }unshi azuzuwan (rukunin) mutane a zamantakewar al‟ummar Hausawa ta fuskar matsayi, jinsi, daraja da kuma ilmi. A wani sashen kuwa a za a duba yadda zamantakewar aure da tsarin iyali na Hausawa ke gudana. Sauran batutuwan kuwa sun ha]a da ; Al‟adun Haihuwa da reno (tarbiyya), Taubasantaka da „yanuwantaka da kuma ma}wabtaka a zamantakewar Hausawa. A }arshe kuma a kawo al‟adun mutuwa da tsarin rabon gado da kuma gurbin barkwanci a zamantakewar Hausawa.
Manufar wannan kwas ita ce a samar wa da ]alibai ko masu karatu bayanai da za su ba su haske ko masaniya a kan batutuwan da suka shafi al‟adun zamantakewar Hausawa, kama da tsarin zamantakewar iyali da haihuwa da tarbiyya da zumunci ma}wabtaka da kuma al‟adun mutuwa.
Wannan kwas ya }unshi fasali guda uku muhimmai, kuma kowane daga cikin fasullan suna ]auke ne da kashi hu]u zuwa biyar, wannan ya bayar da jimlar kasusuwan guda goma sha hu]u a gaba]ayan kwas ]in. A cikin kowane kashi akwai tambayoyin auna fahimta da aka yi zuwa ga ]alibai domin su zamar masu wata kafa ta auna fahimtarsu zuwa da darussan.